Sanatan Kano ta Tsakiya Rufa’i Sani Hanga, ya bayyana cewa waɗanda suka sauya sheƙa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC a jihar da kansu za su dawo, saboda matsalar da za su fuskanta a APC.
Sanata Rufa’i Hanga ya bayyana ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf, daga jam’iyyar NNPP a matsayin ƙundumbalar siyasa da za ta kai shi ta baro.
Ya ce gwamnan ma kansa zai yi wuya ya samu tikitin takara a sabuwar jam’iyyar da ya shiga.
A tattaunawarsa da manema labarai ranar Lahadi, Sanata Hanga ya ce ya taɓa gargadin gwamnan kan kada ya yi hakan, amma bai saurare shi ba.
A makon da ya gabata ne Gwamnan tare da wasu ’yan majalisar dokokin jiha da kuma wasu masu riƙe da mukaman siyasa sun sanar da ficewarsu daga NNPP, suna danganta hakan da rikice-rikicen cikin gida da kuma sabanin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar.
