Kungiyar samarin Tijjaniyya ta kasa karkashin jagorancin sheikh Barrister Habibu Muhammad Dan Almajiri Fagge, ta gudanar da taron ta domin yiwa kasa da kuma jihar Kano addu’ar samun lafiya duba da kalubalen rashin tsaron da ake samu a wasu wurare.
Da yake zantawa da Premier radio Barista Habibu Dan Almajiri Fagge, ya bayyana cewa addu’a ita ce hanya daya tilo da za a bi domin magance ko wacce matsala data addibi al’umma.
Ya kuma yi kira ga al’umma dasu ci gaba da sanya idanu tare da tallafa wa yinkurin hukumomin tsaro na tabbatar da zaman lafiya a koda yaushe.
Taron ya samu halartar limamai daga sassa daban daban da kum al’umma da dama.
