Sabuwar taƙaddama ta ɓarke tsakanin dillalan mai da shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, bisa zargin da ya yi musu na ƙin huldar ciniki da matatarsa.
Aliko Ɗangote ya ce ya na da mai a ƙasa da zai wadaci kasar na tsawon kwana goma sha biyu babu katsewa, ko da kuwa matatar ba ta ƙara yin aiki ba, sai dai ’yan kasuwa sun ce dole sai ya sayar musu da sauƙi, saboda man nasa ya yi tsada.
Tun lokacin da matatar Ɗangote ta fara tace man fetur ake taƙaddama tsakanin kamfanin da jami’an gwamnati da yan kasuwa.
Yan Nijeriya sun yi fatan cewa fara aikin wannan katafariyar matata zai samar da wadataccen mai mai araha a ƙasar nan, sai dai kuma murna na neman komawa ciki, domin maimakon farashin ya sauka, sai tashin gwauron-zabo yake yi.
Yan Najeriya dai sun ce babbar buƙatarsu ita ce sauƙin mai da kuma wadatuwarsa, ba irin wannan rikici da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa ba.
Da alama dai tsuguno ba ta ƙare ba, domin yayin da Ɗangote ke bugun ƙirji cewa matatarsa kaɗai ta isa ta wadatar da Najeriya da man da ake buƙata, ’yan kasuwa sun dage cewa dole sai yayi musu saukin farashi kafin su saya.