
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Karɓi Sabon Jirgi sama da shugaba Tinubu ya saya bayan kwashe watanni ana yi kwaskarima a Afrika ta Kudu.
An sayo jirgin, ƙirar Airbus A330-200 ne a watan Agustan 2024, an kuma gan shi ne a Filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe a Abuja a ranar Laraba.
Jirgin da aka sayo kan Naira biliyan 150 ya dawo gida Najeriya ne bayan kwashe watanni a ƙasar Afrika ta Kudu ana sauya masa launi zuwa launin kore da fari na tutar kasar.
Tun a watan Fabrairun 2025 jirgin ya ke ajiye a filin daga bisani aka fita da shi zuwa ƙasar da nufin yi masa fenti da wasu ‘ƴan gyare-gyare.
Wani jami’i daga fadar da ya nemi a sakaye sunansa ya tabbatar da isowar jirgin ga jarida PUNCH, ya kuma ya ce, nan ba da jimawa ba jirgin zai fara aikin kai-komo da shugaba Tinubu, sai dai babu masaniya kan ko shugaban ƙasar zai yi amfani da jirgin a tafiyarsa ta gaba.
Jirgin na ɗauke da ɗakin bacci da makewayi da ɗakin taro da kuma kayan sadarwa na zamani. Shugaban ya sayo shi ne da nufin maye gurbin tsohon jirgin Fadar, wanda marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ke amfani da shi a lokacin da ya ke kan mulki duba da tsufarsa.