
Hukumar Kula da Aikin Hajji ta kasa NAHCON ta aike da jami’anta zuwa kasar Saudiyya domin tattaunawa da hukumomin kasar kan tsauraran sabbin ka’idojiin da ta fito da su ga maniyata.
Ana hasashen sababbin ka’idojin, ka iya hana maniyyata da yawa damar sauke farali a bana.
Kasar Sudiyya ta ce, sabbin ka’idojin nata bata fito da su, dan ta muzgunawa mahajjata ba, sai dai dan ta basu cikakiyar kulawa da kariya a matsayin su na baki kuma wadanda suka je kasar domin gabatar da ibadar Allah.