Kimanin masu kada kuri’a miliyan 2.7 da aka yi wa rajista a Jihar Anambra za su fita yau Asabar domin zaben sabon gwamnan jihar.
Zaben na yau zai kunshi ‘yan takara daga jam’iyyu 16, amma masana sunyi hasahen fafatawar zata fi tsamari tsakanin ‘yan takara hudu da suka hada da gwamnan mai ci, Charles Soludo na (APGA); George Moghalu na Labour Party (LP); Nicholas Ukachukwu na (APC); da kuma Jude Ezenwafor na (PDP).
Ana kallon wannan zabe a matsayin gwajin amincewa da shekaru hudu na mulkin Soludo yayin da yake neman wa’adi na biyu. Hakazalika, jam’iyyar APC na ganin wannan dama ce da za ta iya fadada tasirinta a yankin Kudu maso Gabas ta hanyar lashe Anambra, wacce ke karkashin APGA tun daga shekarar 2006.
- INEC ta sanar da ranakun zaben cike gurbi ciki har da na Bagwai da Shanono
- NDLEA Ta Kama Ɗan Kasuwan da safarar Kwayoyi 127 a duburarsa
Hakazalika zaben zai gwada tasirin siyasar dan takarar jamiyyar Labour party na zaben shugaban kasa na 2023, Peter Obi wanda shi ne gwamna na farko a karkashin APGA a jihar gabanin zaben 2027.
A daya bangaren kuma, jam’iyyar PDP na ganin wannan dama ce da za ta iya dawo da martabarta bayan rikicin cikin gida da ya raba ta gida biyu tun bayan rashin nasarar da tayi a zaben shugaban kasa na 2023.
Wannan zabe shi ne na farko da za a gudanar karkashin sabon shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan (SAN), wanda aka nada a ‘yan makonnin da suka gabata.
Kungiyoyin farar hula da ‘yan Najeriya da dama sun bayyana wannan zabe a matsayin gwaji na farko ga jagorancinsa gabanin tunkarar zaben shugaban kasa na 2027.
