Kungiyar Kwadago ta kasa (NLC) ta taya daukacin al’ummar Najeriya murnar bikin Sallah Karama, tare da nuna damuwa kan halin ƙunci da matsin tattalin arziki da jama’a ke fuskanta a halin yanzu.
A cikin wani sako na musamman da mataimakin shugaban kungiyar na kasa Kwamared Kabiru Ado Minjibir (Magayakin Minjibir) ya fitar,yace kungiyar ta bayyana cewa tana sane da irin wahalhalu da talakawa ke ciki, amma ta bukaci su da su ci gaba da kasancewa masu hakuri,dajuriya da kuma fatan alheri.
Kwamared Minjibir yace NLC ta jaddada cewa, duk da tsananin kalubalen rayuwa da ake ciki , akwai haske a nan gaba, inda ya nuna kwarin gwiwar cewa wannan hali na ƙunci ba zai dawwama ba, illa zai wuce ya zama tarihi.
Kungiyar ta kuma bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci na Sallah wajen karfafa zumunci, da taimakon juna, da kula da marasa galihu, domin rage radadin rayuwa a tsakanin al’umma.
A karshe, Kwamared Minjibir ya yi addu’ar Allah Ya kawo sauki cikin gaggawa, sannan Ya tabbatar da zaman lafiya, tare da samar da cigaba mai dorewa ga kasa baki daya
