Sarkin ya yi alkawarin shiga tsakani ta hanyar kafa kwamiti da ya hada da kowanne bangare ciki har da gwamnatin Kano.
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II ziyarci unguwannin Rimin Auzinawa da kuma Rimin Zakara da ke Karamar Hukumar Ungogo a ranar Talata.
Sarkin ya kai ziyarar ce don jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma sauran wadanda lamarin na rusau ya rutsa da su.
“Dole ne mu yi wa wadanda suka rasu a addu’a sannan mu jajanta wa iyalan wadanda lamarin ya shafa. Muna fatan wannan ya zama karo na ƙarshe da irin haka za ta sake aukuwa.”
Sarkin ya bukaci mazaunan da su kai zuciya nesa su bai wa mahukunta na shari’a su yi aikin da rataya a wuyansu, yana mai cewa babu abin da rikici zai haifar face ƙarin wahala.
“A duk lokacin da tarzoma ta tashi mutanenmu ne ke kwanana ciki. Babu yadda za a yi zubar da jini ko tashin-tashina su iya warware wannan matsala. Dole ne mu hada kai mu kare rayuwa da dukiyar al’ummarmu.
Sarkin ya hori dukkan bangarorin da lamarin ya shafa su warware tankiya da ke tsakaninsu ta hanyar shari’a tare da gabatar wa kotu ƙwararan hujjoji
A kokarin shiga tsakani don ganin an zauna lafiya, Sarkin ya sanar da kafa wani kwamiti da zai yi ruwa da tsaki da zai hada da wakilan dukkan bangarorin da abin ya shafa da ciki har da Gwamnatin Kano, mahukuntan Jami’ar Bayero da jami’an tsaro da kuma shugabannin yankin.
Sarkin ya ƙara nanata kiran a zauna lafiya yana mai cewa babu wani fili ko wata dukiya da za ta yi daidai da darajar ran dan Adam.
Aminiya ta ruwaito cewa tuni dai kura ta lafa kuma jama’a sun ci gaba da harkokinsu na yau da kullum bayan azamin rikicin da aka yi tsakanin mahukunta da mazauna yankin da ya kai ga rasa rayuka da kuma kone gidan dagacin garin.