Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da samun gagarumar nasara a kokarinta na dakile satar motoci, inda ta samu nasarar kwato motoci hudu da aka sace tare da kama mutane hudu da ake zargi da hannu a lamarin.
Rundunar ta ce wannan nasara ta samu ne sakamakon aiwatar da umarnin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu, na amfani da bayanan sirri da fasahar zamani wajen gudanar da bincike da ayyukan tsaro.
A cewar rundunar, a ranar 7 ga watan Maris din shekarar 2026, jami’an sashen yaki da satar motoci sun tare wata mota kirar Hyundai Elantra mai launin shudi a gadar sama ta Naibawa a Kano.
Motar na hannun wasu mutane biyu, Ibrahim Muhammad mai shekaru 29 daga Minna a Jihar Neja da Ahmed Sani mai shekaru 32 daga Abuja, inda bincike ya tabbatar da cewa motar an sace ta ne daga Abuja, kuma wadanda ake zargin sun amsa laifin.
Haka kuma a ranar 9 ga watan Maris, jami’an sun sake kama Abdulkarim Mamman mai shekaru 30 daga Malali a Kaduna a Kwanar Dawaki da ke kan hanyar Kano zuwa Zariya, yana dauke da mota kirar Honda Civic mai launin toka, wadda ya amsa cewa ya sace ta ne daga unguwar Karkasara a Kano.
Bugu da kari, an kama Yusuf Ali mai shekaru 28 daga Kaduna da ake zargi da hannu a satar mota kirar Toyota Corolla mai launin azurfa da aka sace daga Dutse a Jihar Jigawa.
Rundunar ta kuma ce ta kwato wata mota kirar Nissan Sunny mai launin fari da aka sace daga wani filin ajiye motoci a cikin birnin Kano.
Rundunar ‘yan sandan ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike a kan wadanda ake zargin, kuma da zarar an kammala binciken za a gurfanar da su a gaban kotu.
