Ƙungiyar RSF ta Sudan ta sanar da tsagaita wuta na tsawon wata uku, domin ayyukan jinƙai a yakin da ta ke yi da dakarun gwamnati.
Sanarwar ta zo ne kwana ɗaya bayan da rundunar sojin Sudan ta yi watsi da wani daftarin dakatar da tsagaita wutan da masu shiga tsakani na duniya suka gabatar, tana mai cewa yarjejeniyar ta fifita RSF.
Kwamandan RSF, Mohamed Hamdan Dagalo, ne ya bayyana wannan mataki a cikin wani bidiyo da aka yaɗa.
Yarjejeniyoyin dakatar da yakin da aka rika yi a baya sun rika rushewa kafin su kai ga aiwatarwa, saboda rashin hadin kai daga ɓangarorin da abin ya shafa.
Tun daga barkewar yaƙin basasar a 2023, dubban fararen hula ne suka rasa rayukansu a rikicin da ke ƙara ta’azzara tsakanin RSF da rundunar soji a Sudan.
