 
        Dan takarar jam’iyyar adawa a Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, wanda ya yi iƙirarin lashe zaɓen shugaban kasar yayi kira ga jama’ar kasar da su zauna a gida na kwanaki 3 a matsayi na bijerewa gwamnati.
Bakary ya kira da jama’ar su mayar da garuruwan kasar kufai daga ranar Litinin 3 zuwa Laraba 5 ga watan Nuwamba.
A wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta a ranar Juma’a, Tchiroma ya ce, manufar wannan mataki shine tsayar da harkokin ƙasar gaba ɗaya, domin duniya ta fahimci cewa “muna nuna adawa, kuma ba za mu mika wuya ba.”
Ya buƙaci jama’a da su rufe shagunansu, su dakatar da ayyukansu, su zauna a gidajensu, domin nuna haɗin kai da juna da kuma tunatar da gwamnati cewa “karfin tattalin arziki yana hannun jama’a ne.
Duk a wani sabon mataki na nuna adawa da sakamakon zaɓen da ya ayyana shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya lashe zaben.
Kiran nasa na zuwa ne bayan rikice-rikicen da suka ɓarke bayan zaɓe, wanda ya yi sanadin mutuwar da raunata mutane da dama, tare da kame wasu masu zanga-zanga da yawa a manyan garuruwan kasar.
Tchiroma, ɗan shekara 76, wanda tsohon kakakin gwamnatin ƙasar ne, ya bayyana cewa an ɗauke shi an kai shi zuwa wuri mai tsaro ta hannun wasu sojojin da ke goyon bayansa, wadanda yanzu ke kula da tsaronsa.
A farkon makon nan, gwamnatin ƙasar ta ce Tchiroma Bakary zai fuskanci shari’a bisa iƙrarin nasara da kuma shirya zanga-zanga, wanda ta bayyana a matsayin tayar da fitina.

 
           
           
           
           
         
         
         
         
         
         
           
          