Dakarun Kungiyar RSF ta samu nasarar kwace birnin El Fasher dake yankin Darfur bayan sama da watanin 18 da yiwa birnin kawanya.
Nasara da kungiyar ta tabbata ne bayan da shugaban majalisar mulkin Sudan Abdel Fattah al Burhan ya sanar da cewa, sojin ƙasar sun janye daga Al Fasher, a wani jawabi da ya yi a gidan talbijin din kasar a ranar Litinin.
“Mun yarda mu janye sojoji daga Al Fasher zuwa wani wuri da ya fi tsaro… Zamu dauki fansa, kuma zamu ci gaba da yaki har sai lokacin da aka tsaftace kasar,” in ji shugaban.
Sanarwar ita ce ta farko inda Burhan ya yarda cewa ya rasa Al Fasher, birnin mai muhimmanci da ya kasance ƙarƙashin ƙawanyar rundunar RSF tun watan Mayun shekarar 2024.
Wacce kuma take yaki da sojin gwamnati don kame birnin tun watan Afrilun shekarar 2023.
RSF ta yi shelar samun nasara a birnin a ranar Lahadi.
Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) mai kula da Hijira a ranar Litinin ta bayyan cewa fiye da mutune 26,000 ne suka tsere daga yaƙi a Al Fasher tun ranar Lahadi
Wasu na neman mafaka a wajen birnin ko kuma suka nufi Tawila, da ke da nisan kilomita 70 yamma da birnin.
MDD ta kuma ce, fiye da mutane miliyan ɗaya ne suka tsere daga birnin tun lokacin da aka fara yaƙin yayin da kimanin fararen-hula 260,000 wadanda rabinsu ƙananan yara da yakin ya rutsa da su, ba tare da samun agaji ba, a inda da yawa daga cikinsu suka koma cin abincin dabbobi.
Ƙwace Al Fasher ya baiwa rundunar RSF iko a kan sama da manyan biranen jihohi biyar a Darfur, lamarin da ya ƙarfafa ikonta a Nyala, babban birnin jihar Darfur ta kudu.
A halin yanzu ikon sojin ƙasar ya tsaya ne kawai a arewaci da gabashi da kuma tsakiyar Sudan.
Rahotanni sun ce akwai dubban sojojin gwamnati da har yanzu mayakan RSF suka yi wa kawanya a wajen yammacin birnin.
RSF ta musanta zarge-zargen cewa tana kashe fararen hula, to amma kungiyoyin agaji na fargabar an yi wa kabilun da ba larabawa da suka makale a birnin kisan kiyashi.
Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce kawanyar da aka yi wa birnin na El Fasher tsawon watanni 18, ya jefa mazauna yankin cikin mummunan yanayi na yunwa da cutuka ga kuma tashin hankalin fadan da ake gwabzawa.
