
Kwankwaso na Kano yayin da daya bangaren ya zabi Agbo Major a matsayin sabon shugaba a babban taron jam’iyyar
Rikicin cikin gida na jam’iyyar adawa ta NNPP na ci gaba da kamari, inda a yanzu haka bangarori biyu ke ikirarin iko da jam’iyyar.
A ranar Laraba a jihar Legas daya bangaren jam’iyyar yayi taronsa na kasa aka kuma zabi sabbin shugabannin jam’iyyar.
An kuma zabi Mista Agbo Major a matsayi sabon shugabanta.
Sai dai bangaren kwankwasiyya ya nesanta kansa daga babban taron, a inda Sakataren kwamitin Gudanarwa Injiya Buba Galadima ya ce, taron ba halasatcce bane.
“Ai duk babban taro na jam’iyya musamman Convention, in babu wakilin INEC ba halasaccen taro bane.
“Na biyu da wanne alamar jam’iyya suka yi amfani? Alamar jam’iyyarmu littafi da hular digiri a sama ne, da launi ja, jan aiki da fari, farin ciki da zama lumana.
“Su kuwa a nasu taron sun yi amfani ne da alamar jam’iyya mai kayan maramari ne. INEC kuwa ba ta san da zamansu ba…” In ji shi.
Su kuwa ‘yan daya bangaren jam’iyyar sun ce, taronsu halastacce ne kuma da amincewar Hukumar Zabe ta kasa INEC aka yi shi.
A cewar Injiniya Muhammad Babayo Abdullahi Mataimakin Shugaban bangaren na kasa mai kula da shiyyar Arewa a hirarsa da BBC. Bangaren Kwankwasiyya shirme suke yi.
“Kowa ya sani lokacin da aka yi rajistar wannan jam’iyya da logon kayan marmari da kuma launin kore da shudi aka yi mata rajista.
“Kuma a cikinta suka zo suka same mu, kuma a ciki muka sahele musu suka tsaya da ‘yan takarakarunsu da sauransu.
“Satifiket din wannan jam’iyyar yana hannun kawo yanzu. Kuma ko a Kano da za a yi zaben kananan hukumomi Kotu cewa ta yi a hannunmu za a karbi ‘yan takarkaru ba a wurinsu ba.” In ji Babayo
Wannan rikici na zuwa ne a lokacin da jam’iyya mai mulki ta APC ke kara karfi don tunkarar babban zabe mai zuwa.