Ana fargabar rikicin da ke ƙara taɓarɓarewa tsakanin ƙasashen Iran da Isra’ila zai iya kawo tangarɗa wajen samar da man fetur daga yankin Gabas ta Tsakiya.
Hakan ya biyo bayan yunkurin da kasar Iran tayi na rufe mashigar Hormuz, wadda take zama babbar hanyar safarar man fetur tsakanin yankunan duniya.
Wani masanin tattalin arziki Dakta Nasir Turawa ya bayyana cewa idan aka rufe Hormuz ba shakka za a iya samun ƙarancin man fetur, wanda hakan zai janyo karin farashi a wasu sassan duniya.
Ya kara da cewa idan hakan ta faru gwamnatocin ƙasashen dake iya samar da man fetur da kansu zasu iya samun karin kudin ta dalilin haka.
Dakta Nasir Turawa ya ja hankalin gwamnatin Najeriya kakan cewa idan aka tsinci kai a irin wannan yanayi talaka kan shiga halin kaka na kayi, ya kamata gwamnatin ta baiwa talakawa tallafi na kudi da rage kudin ababen sufuri a fadin kasa baki daya
