Mai ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro Nuhu Ribadu, ya ziyarci garin Kwantagora, don ganawa da shugaban ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Neja, Bishop Bulus Dauwa Yohanna.
Ganawar ta ƙunshi duk iyaye da malaman Makarantar St. Mary da ƴanbindiga suka sace.
Jakadan Chaina ya ziyarci Ribadu a Abuja
Shugaban Kasa Ya Umurci Hukumomin Tsaro Su Kubutar da Daliban da Aka Sace a Kebbi
Sace ɗaliban ya haifar da ruɗani a Najeriya, musamman faruwarsa ƴan kwanaki bayan sace ɗaliban jihar Kebbi.
Adadin ɗaliban da aka sace ya janyo saɓani tsakanin gwamnati da hukumar makarantar. Makarantar dai ta ce ɗalibai fiye da 300 aka sace, yayin da gwamnatin jihar Neja da ƴansanda suka nuna shakku game da alƙaluman.
