
Karmin Ministan Tsaron Dakta Bello Muhammad Matawalle, ya kaddamar da jerin sabbin motocin soji masu amfani da iskar gas na CNG.
Wannan wani babban mataki ne da ke nuna kokarin gwamnatin tarayya na kawo sauyi a fannin makamashi a harkokin tsaron kasa.
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a sansanin sojoji na Mogadishu da ke birnin tarayya Abuja.
A cewar wata sanarwa da mai taimaka masa kan kafafen yada labarai, Ahmad Dan-Wudil ya fitar a ranar Talata, Matawalle ya bayyana wannan mataki a matsayin gagarumar nasara wajen kirkire-kirkire, rage yawan kashe kudin aiki da inganta amfani da makamashi a harkokin sufurin rundunar soji.
Ministan ya bayyana cewa wannan shiri na amfani da CNG zai rage dogaro da man fetur, ya rage fitar da hayakin da ke gurbata iska, kuma zai taimaka wa Nijeriya wajen cimma kudirorinta na kare muhalli a matakin duniya.
Ministan ya bukaci a gaggauta kafa tashoshin zuba gas na CNG a dukkan sansanonin soji domin tabbatar da ci gaba da amfani da motocin.
Haka zalika, ya jaddada bukatar horar da jami’an soji yadda ya kamata domin su iya kula da kuma gudanar da motocin CNG yadda ya dace.