Za a kammala aikin hanyar jirgin ne daga wani rance daga kasar Chaina wanda za a soma nan ba da dadewa ba
Bankin Raya kasa na China ya amince da bayar da Dala miliyan 254.76 kimanin Naira 393,265.37domin kammala aikin jirgin kasa daga Kano zuwa Kaduna.
Bankin ya amince ya ba da rancen ne gabanin ziyarar da Ministan Harkokin Wajen China, Mista Wang Yi, zai kawo Najeriya a wannan makon, inda ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba.
Aikin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Kaduna mai nisan kilomita 203 zai ci kudi Dala miliyan 973, kuma zai sada su da Abuja.
Aminiya ta rawaito cewa, aikin ya samu tsaiko amma Bankin na China ya ba da tabbacin samar da isassun kudade domin tabbatar da kammalawa cikin lokaci.
Ana sa ran sufurin jirgin kasa daga Kano zuwa Abuja sai saukaka zirga-zirgar mutane da harkokin kasuwanci tsakanin sauran sassan Najeriya da Kano, cibiyar kasuwanci