
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Talata 15 ga watan Yuli a matsayin ranara hutu a duk fadin kasar.
Gwamnatin ta ayyana hakan ne domin alhinin mutuwar tsohon shugabana kasa Muhammadu Buhari da ake sa ran yin jana’izarsa a gobe Talata a Daura.
Tsohon shugaban wanda ya rasu a wani asibiti a birni Landan a ranar Lahadi ana sa ran isowar gawarsa Katsina domin yi mata jana’iza da kuma binneta a goben. Ana kuma sa rai shugaban kasa Bola Tinubu zai halarta.
Tuni manyan mutane daga ciki da kuma wajen kasar suka soma hallara a garin Daura don yin ta’aziya
Sanarwar da Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan, Dakta Magdalene Ajani ta fitar ta ce an ayyana hutun ne domin girmamawa da kuma tuna gudunmawar da marigayi Buhari ya bayar a fannin dimokuradiyya da ci gaban ƙasa.
Kazalika, sanarwar ta buƙaci ’yan ƙasa da su yi amfani da wannan hutu wajen tunawa da rayuwar tsohon shugaban ƙasar.
A yayin da Gwamnatin Tarayyar ke ci gaba da yi wa mamacin addu’a, ta sake miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, al’ummar Jihar Katsina da kuma ɗaukacin ’yan ƙasa dangane da wannan babban rashi.