
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya dakatar da rangadin da yake yi a Dawakin Tofa da Tofa da Rimin Gado sakamakon rasuwar Aminu Dantatta.
Sarkin ya kuma ba al’ummar garuruwan ba da zai je rangadain da su yi hakuri.
Sarkin ya isa garin Dawakin Tofa a ranar Juma’a ya wayi gari ranar Asabar don soma rangadi a garin da kuma Tofa sannan ya wuce Rimin Gado.
Ya kuma ce zai cigaba da rangadin ne bayan share makokin attajirin