Rashin wuta: Think.go ta tallafawa Kano, Jigawa da Yobe da burtsatse masu amfani da hasken rana

0
143

Kungiyar Think.go da hadin gwiwar hukumar yaki kwararowar Hamada (Great Green Wall Agency) ta samar famfunan ruwa masu amfani da hasken rana a garuruwa uku dake Kano, Jigawa da Yobe.

Kungiyar ta samar da famfunan ne domin magance matsalar karancin ruwa da yankunan suka dade suna fuskanta. Yankunan da aka gina fanfunan sun hada da Nayi Nawa Bukka shida a karamar hukumar Nguru da kauyen Dan Tanoma dake karamar hukumar Gumel sai Dakata Kawaji a karamar hukumar Nasarawa a nan Kano.

Da yake jawabi yayin kaddamar da famfunan babban darakta a Thin.go Climate Conscious Atmosfair, Alhaji Abdurahman Bawa, ya ce wannan yana cikin aikin su na bunkasa rayuwa al’umma da sana’o’I da kuma kuma bangaren muhalli.

Ya ce shirin ba iya tsaftataccen ruwan sha zai samar ga mutane da dabbobi ba, zai kuma taimaka wajen yin amfani da hanyoyin makamashi na zamani da duniya ke amfani da shi domin magance matsalar sauyin yanayi.

Wasu daga cikin shugabanin al’ummomin yanklunan da suka amfana da shirin sun bayyana jin dadin su.

Shima shugaban karamar hukumar Gumel Alhaji Lawan Ya’u Abdullahi ya bayyana jin dadin sa inda ya bukaci wadanda suka amfana suyi amfani dasu yadda ya dace.

A nasa jawabin darakta mai kula da dajuka da kasa, na hukumar yaki da kwararowar Hamada, Eng Ahamad Bagudo, ya samar da rushon girki domin rage sare bishiyu da kare mata daga cutukan dake tattare da amfani da itace.

Eng Ahamad Bagudo, ya ce a koda yaushe mata nayin girki kuma hakan yana shafar lafiyar su sakamakon shaker hayakin girki, sannan matsalar tana haddasa gurbatar muhali.

Da suke jawabi, manaja a bangaren tsara manufofi Eng Orezi Omeatu da Eng Abdulrasheed da Ahmad Imam, manaja a bangaren kasuwanci, na (Atmosfair Climate And Sustainability), sun ce duk da cewa Atmosfair ce ke samar da rishon girkin amma reshen kamfanin a Najeriya yana samar da nashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Captcha verification failed!
CAPTCHA user score failed. Please contact us!