
Sarkon Kano Muhammadu Sunusi yayin karbar gaisuwa daga dagatai da masu unguwanni a ragandin
Daga Khalil Ibrahim Yaro
Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya ziyarci wasu Kananan Hukumomin jihar a cikin wani shirin rangadin gundumomin masarautar jihar
Sarkin ya soma rangadin da sauka a garin Dambatta a ranar juma’a inda ya jagoranci sallar Juma’a a Babban Masallacin Juma’a tare da gabatar da Huduba mai Ratsa jiki kan al’umma su mayar da hankali su kuma ji tsoron Allah tare da kyautata dabi’un su.

Da dare kuma an gudanar da Majigi a Kofar Gidan Hakimi inda sarki ya sauka wanda mutane da yawa suka halarta.
Wayewar garin Asabar Sarki ya kaddamar da rangadin a wani babban taro a kofar gidan hakimin a gaban daruruwan jama’a da suka zo daga sassa daban-daban na karamar hukumar.

Kafin jawabinsa na kadamarwar, Sarki ya karbi gaisuwa daga ‘yan majalisarsa da hakimai da dagatai da masu unguwanni da kuma manyan jami’an karamar hukumar karkashin jagorancin shugabanta da kuma sauran masu fada a ji.
An kuma gudanar da wasan kwakwayo na fadakarwa da wakokin yabon Manzo Sallallahu alaihi wasallama da kuma na sarki.

Masanin Tarihi Ibrahim Ado Kurawa ya gabatar da takaitaccen tarihin mai martaba sarki da salsalarsa da kuma irin nasarorin da samu a rayuwa domin zama abin koyi.

A jawabinsa na kaddamarwa mai martaba sarki ya yi magana kan muhimman al’amura da suka shafi al’umma da kuma zamantakewa ciki har da batun tsaro da bukatar shuka bishiyoyi don maganin kwararowar hamada da kula da lafiyar mata da yara da mace-macen aure da kuma gujewa shaye-shayen miyagun kwayoyi na matasa da kuma matan aure.

Sannan sarkin ya bayyana muhimmancin garin Danbatta a gare shi da kuma dalilin da ya sa yake soma rangadinsa daga can.
Sarkin ya kai irin wannan ziyarar rangadi a Makoda a maraicen ranar Asabar, ya kuma je garin Kunya a ranar Lahadi da safe sannan ya wuce Minjibir da maraice. A ranar Litinin kuma ya je Ungoggo da garin Zaura Babba.

A dukkanin garuruwan da sarki ya ziyarta ya samu kyakkyawan tarba da kuma maraba a inda dubban mutane maza da mata yara da manya suka yi dafifi zuwa tarbar mai martaba sarki a kan hanyarsa da kuma inda aka yi tarukan.

Ana sa ran sarkin zai cigaba da rangadin zuwa sauran kananan hukumomin 38 masu gundumomin hakimai 48 na masaurautar Kano a wani lokaci nan gaba.