
A duk ranar 9 ga watan Satumba kowacce shekara ake tunawa da ranar kare ilmi daga hare-haren ta’addanci a duniya, domin jaddada muhimmancin tabbatar da tsaron makarantu da ilimi ga yara da matasa.
An fara bikin wannan rana ne a shekarar 2019, bayan Majalisar Dinkin Duniya ta ba wa hukumar bunkasa ilmin kimiyya da al’adu ta UNESCO tare da asusun tallafawa yara na UNICEF damar wayar da kan duniya kan illolin hare-haren ta’addanci a fannin ilmi.
Rahotanni daga Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa tsakanin shekarar 2022 da 2023 an kai hare-hare kusan 6,000 a makarantun duniya, inda aka kashe dalibai fiye da 10,000 ko aka yi garkuwa da su.
A shekarar 2024 kadai an samu karin hare-hare a makarantu da kashi 44 cikin 100.
Kasashen da wannan matsala ta fi shafa sun hada da Yankin Gaza dake fama da matsanancin hare-haren ta’addanci daga Isra’ila, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, Somalia, da Najeriya.
Dr. Mubarak Saulawa, malami a Tsangayar Ilmi ta Jami’ar Bayero, Kano, ya bayyana cewa hare-haren ta’addanci a fannin ilmi na da mummunan tasiri, musamman wajen tilastawa yara barin makarantu.
A bangaren sa, masanin tsaro Bala Lawan Kofar Na’isa ya bayar da shawarar daukar matakai masu karfi don magance wannan matsalar, musamman a Najeriya. A Najeriya, musamman a yankin Arewa, matsalar tsaro ta yi matukar tasiri wajen hana yara samun ilmi, musamman a jihohin Borno, Yobe, Zamfara, Katsina da wasu yankuna da dama.