
Daga Khalil Ibrahim Yaro
A Dawakin Tofa ta kama ‘yan caca da kuma masu wasanin gem a Karakashin ‘operation gyara kayanka don gabatowar watan azumi
A karkashin wannan shirin Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta reshen Karamar Dawakin Tofa sun samu nasarar wargaza wasu masu yin caca a wani gida da kuma masu gem inda ake tara yara.
A hirar wakilinmu da Mataimakin Babban Kwamandan Hisba Dakta. Mujahideen Aminuddeen ne ya ce, karatowar azumi zai sa su kara zage damtse wajen ganin an dakile irin wannan ayyauka na badala.
“Wannan abin takaici ne watan Ramandan ya karato, wanda kamata yara su mayar da kai wajen karatu, ko kuma iyaye su ajiye wannan yara a gabansu domin kula da tarbiyar su tare da koya musu sana’a, domin Idan aka bar yaran suka girma ba tarbiya, to za su zama barazana ga al’umma”. In ji shi.