
Wani dan bindiga ya hallaka wasu ma’aikatan ofishin jakadancin Isra’ila mace da namiji a Washington babban birnin Amurka.
Danbindigan ya bude wa ma’aikatan wuta ne a daidai lokacin da suke fitowa daga wajen wani taro da suka halarta a wani gidan adana kayan tarihi na Yahudawa a birnin.
Babu wasu cikakkun bayanai game da wannan hari a yanzu, amma ‘yansanda sun tabbatar da cewa mutumin da ake zargi da bude wa ma’aikatan biyu wuta, ya shiga hannu.
‘Yansandan sun ce mutumin wanda sunansa Elias Rodriguez, mai shekara 30, ya rika furta kalaman ‘yanci ga Falasdinawa a lokacin da aka kama shi.
Shugaban kungiyar Yahudawa da ke Amurka ya ce, kungiyarsa na gudanar da wani taro ne a dakin adana kayana tarihin lokacin da aka kai harin.