A yau Lahadi ne Qatar, za ta karɓi baƙuncin ƙasashen Larabawa Musulmi, domin tattaunawa game da harin da Isra’ila ta kai babban birninta a Talatar da ta gabata.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Majed Bin Muhammad Al-Ansari, ya shaidawa kamfanin dillancin Labaran Qatar cewa taron zai tattauna daftarin ƙuduri game da harin Isra’ila a Doha, wanda aka gabatar gabanin taron ministocin harkokin wajen ƙasashen Larabawa Musulmi.
A cewar Majed, taron a daidai wannan lokaci yana da matuƙar muhimmanci, wanda hakan ‘yar manuniya ce da ke alamta yadda ƙasashen Larabawa Musulmi ke marawa Qatar baya.
A ranar 9 ga watan Satumbar nan ne, Isra’ila ta kai hari ta sama a Doha babban birnin Qatar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar masu tsaron lafiyar jagoran Hamas Kahlili Al-Hayya, su uku da ɗan sa, da kuma wani jami’in tsaron Qatar.
Sai dai a ranar Asabar 13 ga watan Satumbar, 2025, Ministocin harkokin wajen Faransa, Jamus da Birtaniya sun yi Allah wadai da hare-haren saman da Isra’ila ta kai a birnin Doha.
A wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, ministocin sun yi gargaɗin cewa harin ka iya kawo cikas ga ƙoƙarin cimma yarjejeniyar sakin dukkan fursunonin da aka kama tare da kawo ƙarshen yaƙin na Gaza.
