Gwamnatin Tarayya ta ayyana masu garkuwa da mutane da sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a matsayin ’yan ta’adda a hukumance, matakin da ke nuna ƙarin tsanani da sauyin dabaru a yaƙin da ake yi da rashin tsaro a ƙasar.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na ƙarshen shekara da aka gudanar a Abuja.
A cewarsa, wannan mataki yana nuna sabon salo wajen tunkarar ’yan bindiga da sauran masu aikata laifukan ta’addanci, inda daga yanzu za a ɗauke su a matsayin masu aikata manyan laifuka tare da hukunta su bisa dokokin yaƙi da ta’addanci.
“Duk wata ƙungiya ko mutum da ke ɗauke da makamai, yana satar mutane ko razanar da al’umma, daga yanzu za a ɗauke shi a matsayin ɗan ta’adda,” in ji ministan.
Idris ya ƙara da cewa wannan sabon tsari zai ƙara ƙarfafa musayar bayanan sirri da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, lamarin da zai ba su damar ɗaukar mataki cikin gaggawa da karsashi.
Ya kuma sanar da shirin tura ƙarin jami’an tsaro zuwa dazuka da yankuna masu nisa, inda ’yan ta’adda ke amfani da su a matsayin maɓoya.
A cewarsa, aikin zai haɗa da sa ido, tattara bayanan sirri daga cikin al’umma, da gaggawar kai farmaki domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
