
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauya sunan Jami’ar gwamnatin tarayya ta Maiduguri UNIMAID zuwa sunan marigayi Muhammadu Buhari.
Wannan na zuwa na zuwa yayin taron majalisar zartarwa na musamman da aka gudanar tare da addu’o’i ga marigayi shugaba Buhari a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Shugaba Bola Tinubu ne ya jagoranci taron wanda shugabannin majalisar tarayya da wasu daga cikin iyalan marigayin suka halarta.
Tsohon shugaban ƙasar ya rasu ne ranar Lahadi a wani asibiti a Landan bayan fama da jinya.
An kuma binne shi ranar Talata a garin Daura na Jihar Katsina