Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jaddada tabbatar da kudirin gwamnatinsa na tallafawa hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano.
Gwamna Yusuf ya yi wannan alkawari ne yayin da ya karbi bakuncin matar Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda (IGP), Mrs. Elizabeth Kayode Egbetokun, wadda ta jagoranci mambobin kungiyar matan jami’an ‘yan sanda (POWA) a ziyarar ban girma zuwa ofishinsa.
Gwamna Yusuf ya bayyana yadda gwamnatin sa ke ci gaba da baiwa ‘yan sanda gudunmawa wajen ayyukansu yadda ya kamata, musamman ta hanyar samar da kayayyakin aiki da motoci.
Ya kuma nanata cewa tsaron Jihar Kano na daya daga cikin manyan muradun gwamnatinsa.
Ya ce za su ci gaba da tallafawa ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi domin ci gaban al’umma da walwala.
Gwamnan ya yaba da jajircewar Mrs Elizabeth Egbetokun, wajen inganta rayuwar jami’an ‘yan sanda da iyalansu.
Haka zalika gwamna Abba Kabir Yusuf ya baiwa kungiyar kyautar fili da tallafin kudi domin gina sakatariyar ofishin POWA a Kano.
A nata bangaren shugabar kungiyar mata ‘yan Sanda POWA, Mrs. Elizabeth Kayode Egbetokun, ta bayyana cewa ziyarar tasu ita ce sanar da gwamnan ayyukan POWA a Kano, wanda ya hada da bada tallafi da kaddamar da cibiyar kiwon lafiya a Panshekara.
Ta yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa ci gaban da ta samu wajen karfafawa mata kuma ta yi kira a kara hadin gwiwa domin inganta rayuwar tattalin arzikin mambobin POWA, domin tabbatar da makomar iyalansu.