Aminu Abdullahi Ibrahim
Albasar hadin gwiwa da Ibsar International Foundation da King Salman Humaniterian Center sune suka dauki nauyin duba daliban.
Kuma an dauko su ne daga makarantu 82 na Firamare da sakandire na jihar Kano.
An baiwa daliban da aka duba magani kyauta da gilashi, yayin da wasu aka yi musu tiyata.
Da yake jawabi yayin rufe shirin a makarantar Dandago, wakilin gidauniyar Albasar, Yusuf Ahmad ya ce sun raba gilashi da magunguna fiye da dubu 4.
Wasu daga cikin Malaman makarantun da aka zabo daliban sun bayyana mana irin matsalolin da wasu daliban ke fama da su na rashin gani sosai.
Suma iyayen daliban da suka amfana da wannan shirin na duba lafiyar idanu kyauta da gidaunaiyar Albasar da Ibsar suka gudanar a Asibitin Makka sun bayyana mana yadda suka ji.
Gidauniyar Albasar da sauran kungiyoyin da suka dauki nauyin shirin sunce zasu cigaba da duba lafiyar idanun dalibai da basu magani kyauta a Jihar Kano.
Taron ya samu halartar mutane daban ciki har da Ofishin jakadanci kasar saudia dake nan Kano.
