Kungiyar masu hada magunguna ta kasa reshen Kano (Pharmaceutical Society of Nigeria) ta duba marasa lafiya fiye da dubu 3 a wani bangare na taron shekara da take gudanarwa.
Ta gudanar da duba marasa lafiyar a babban Asibitin Dawakiji dake Lahadin Makole a karamar hukumar Dawakin Kudu.
Shugaban kungiyar reshen Kano Pharm. Murtala Isah Umar, ya ce a bana sun samu tallafi daga kungiyoyi daban-daban.
”Mun samu tallafi daga Albasar masu Asibitin Mecca, da hukumar dake gano masu tarin fuka, Society For Family Health, da A.A Zaura Foundation, da Els da Vision Spring,”
Duk sun taimaka mana da magunguna da likitoci,” a cewar sa.
Ya ce an samu fiye da mutum dubu 1000 masu hawan jini da aka baiwa magani da masu ciwon ido 600 inda aka baiwa 150 daga cikin Glass kyauta.
Ya kara da cewa an samu mutum 85 masu yanar ido anyi musu aiki kyauta a Asibitin Mecca da masu cutar Tuberclosis 28. Ya ce an duba masu Maleria fiye da dubu 1000.
Ya ce duk shekara suna zabo guraren da suke nesa da manyan asibitoci da cibiyoyin lafiya tare da tallafa musu.
Ya ce duk wadannan abubuwa sun yi su ne kyauta kuma an samu cikowar mutane daga sassa daban-daban.
Wasu da suka amfana sun bayyana farin cikin da godiya bisa yadda aka duba su tare da basu magani kyauta.
Haka zalika sun godewa kungiyar ta
Pharmaceutical Society of Nigeria Kano Branch.
Wannan dai na cikin bikin da kungiyar take gudanarwa a nan Kano na Shekara-shekara.
