Ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN ) reshen Jihar Filato ta zargi wata ƙungiyar ‘yan bindiga da ke aiki a ƙauyen Izovo, gundumar Miango ta ƙaramar hukumar Bassa, da kai hari kan makiyaya a ranar Asabar, lamarin da ya yi sanadin ɓacewar makiyaya uku tare da kashe shanu biyar.
Shugaban MACBAN na jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a Jos ranar Lahadi.
Ya ce makiyayan na gudanar da harkokinsu na halal ne lokacin da ‘yan bindigar, waɗanda ya bayyana a matsayin ‘yan sa-kai na Irigwe, suka kai musu hari kwanton bauna.
Ya bayyana harin a matsayin barazana ga rayuwar makiyaya Fulani da kuma hatsari ga kokarin samar da zaman lafiya a jihar.
Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike tare da kamo waɗanda ke da hannu a harin domin gurfanar da su a gaban kuliya, yana mai gargadin cewa gazawar daukar mataki na iya ƙara ta’azzara rikici.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar, Alabo Alfred, da jami’in yaɗa labarai na rundunar Operation Enduring Peace, Kyaftin Polycarp Oteh, bai yi nasara ba, domin ba su amsa kira ko sakonnin WhatsApp da aka tura musu ba.
