
Daga Aisha Ibrahim Gwani.
Wata kanwa ta kashe yayarta sakamakon sabanin da suka samu kan kudin Tumatiri da Barkono na kimanin na Naira 800.
A sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar ‘Yansanda jihar, Olayinka Ayanlade ya fitar a ranar Talata ya ce, lamarin ya faru ne a garin Akure babban birinin jihar Ondo wata Asabar na farkon watan Satumba.
Kakakin ya kuma ce, an cafke matar da ake zargi mai suna Iluyemi Bosede bisa zargi, kan kisan yayarta Tewogboye Omowumi bayan ta tureta a yayin wata sa-in sa da ita ta kuma faɗi a ƙasa, daga bisani ta rasu.
“Binciken farko ya nuna cewa Iluyemi Bosede ta je gidan yayarta, Tewogboye Omowumi mai shekaru 35, domin karɓar bashin N800 na kudin tumatir da barkono. Sai dai rigimar da ta barke taskaninsu a matsayin ƙarama sai ta rikide zuwa tashin hankali, inda ake zargin Bosede ta ture marigayiyar har ta fāɗi ƙasa.
“Duk da cewa an garzaya da marigayiyar asibiti, likitoci sun tabbatar da mutuwarta tun kafin a fara ba ta wani taimako. Wannan lamari ya nuna yadda ƙaramin sabani zai iya rikidewa zuwa mummunar husuma idan ba a magance shi cikin lumana ba,” in ji shi.
Rundunar ta tabbatar da cewa an kama Bosede wadda ake zargi kuma tana tsare yayin da rundunar ata take gudanar da bincike kan lamarin. Za kuma a gurfanar da ita a gaban kotu bayan kammala binciken,