
Shugabannin jam’iyyar PDP na Arewa sun yanke shawarar mayar da shugabancin jam’iyyar na kasa zuwa yankin Arewa maso Yamma a wani mataki na hada kan jam’iyyar gabanin Babban taron.
Shugabannin jam’iyyar sun fitar da wannan matsaya ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na yankin Arewa da aka gudanar a Abuja a karshen mako.
Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun takun saka dangane da babban taron kasa na jamiyyar da za a gudanar a watan Nuwamba a birnin Ibadan na jihar Oyo,
Jaridar punch ta rawaito cewa shugabannin sun amince yankin ya samar da shugaban jam’iyyar na kasa.
Yayin da sauran shiyyoyin a cikin wannan mako za su yanke shawara kan wadanda za su amince da su kan sauran muhimman mukamai.
Ana rade-radin cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, da tsohon ministan ayyuka na musamman Tanimu Turaki (SAN), da kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi cikin su shiyyar za ta fitar daya.
Wani babban jami’in jam’iyyar ya tseguntawa jaridar cewa, akwai yiyuwar Turaki ya zama shugaban jam’iyyar PDP na kasa, inda ya ce ya samu goyon bayan manyan masu ruwa da tsaki ciki har da gwamnonin da suka rage a jam’iyyar a yanzu.
A watan Nuwamba ne jamiyyar ke fatan gudanar da babban taron ta na kasa, wanda kuma ake hasashen samun sauyi a jamiyyar bayan taron, duk da cewa wasu daga cikin yayan jamiyyar na adawa da taron.