
Firayim Ministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, ya bayyana harin Isra’ila a Doha a matsayin ta’addanci, kuma lallai a hukunta ta.
Shugaban ya kuma bukaci al’ummar duniya da su daina nuna bambancin wajen hukunta Isra’ila bisa manyan laifukan da ta ke aikatawa.
“Harin da Isra’ila ta kai ranar 9 ga Satumba kan jagororin kungiyar Hamas a babban birnin Qatar ya saba wa dokokin kasa da kasa.” In ji shugaban, a jawabin da ya gabatar a taron share fagen taron kolin kasahen Larabawa da Musulmi a Doha da aka fara yau Litinin.
Shugaban ya kuma jaddada cewa wadannan hare-hare ba za su dakatar da Qatar da Masar da Amurka ba daga shiga Tsakani domin kawo karshen yakin Gaza.
Rahotanni sun nuna cewa jiragen yakin Isra’ila sun harba makamai masu linzami sararin samaniyar Saudiyya kafin su kai hari a birnin Doha.Harin ya auka kan wani yanki inda aka kashe ’yan Hamas biyar da kuma wani jami’in tsaron Qatar, duk da cewa manyan shugabannin Hamas sun tsira.
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah-wadai da harin baki daya.