Gwamnatin Tarayya Ta Fara Aikin Samarwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano wutar lantarki ta hasken rana mai karfin Mega Watt 4.
Hukumar Kula da Harkokin Makamashi ta Ƙasa ta ce ta bayyana fara shirin samar da wutar lantarki ta hasken rana ga asibitin a ranar Talata.
Shugaban Hukumar Dakta Mustapha Abdullahi, ya ce aikin na daga cikin manufofin Shugba Tinubu na Renewed Hope Agenda.
“Shirin zai bai wa asibitin damar rabuwa da dogaro da layin wutar lantarki na ƙasa baki ɗaya… tsarin zai kuma kawo ƙarshen matsalar yawan yanke wuta a asibitin, lamarin da ya haddasa asarar rayukan marasa lafiya a lokacin da ayyukan asibitin suka tsaya cak”. In ji shi.
Rahotanni sun nuna cewa wannan shi ne karo na farko da asibitin zai samu tsarin wutar lantarki da zai rike shi gaba ɗaya ba tare da dogaro da wutar lantarkin ƙasa ba.
