
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta soke duk wani lasisi da aka bayar ga masana’antu dake fadin jihar, bayan gano cewa wasu daga cikinsu suna amfani da damar lasisin ne wajen karya dokar aikin tsaftar muhalli na ƙarshen wata-wata.
Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta jihar, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano, jim kaɗan bayan karɓar rahoton da ke nuna cewa wasu masana’antun na ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da dokar hana aiki a lokacin tsaftar muhalli.
Dakta Dahir ya ce, matakin soke lasisin zai taimaka wajen tabbatar da bin doka da kuma dakile duk wani yunƙurin karya ƙa’idar tsaftar muhalli da gwamnati ta tanada.
Kwamishinan ya bada tabbacin cewa ma’aikatar za ta ci gaba da bakin kokarin su domin tsaftace jihar nan a koda yaushe.