
Jihar Kano ta zama kan gaba a sakamakon jarrabawar kammala sakandire ta 2025 (SSCE) da Hukumar NECO ta fitar.
Shugaban hukumar, Farfesa Ibrahim Wushishi, ne ya bayyana haka a Minna ta jihar Neja, yayin da yake sanar da sakamakon jarrabawar ta wannan shekara.
“Dalibai 68,159 daga jihar Kano ne suka samu nasara a darussa biyar ciki har da Turanci da Lissafi.
“Jihar Legas ta zo a matsayi na biyu da dalibai 67,007, sai kuma jihar Oyo da ta zo ta uku da dalibai 48,742.”. In ji shi.
Da yake bayyana farin cikinsa kan wannan gagarumar nasara, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya danganta hakan ga matakan da gwamnatinsa ta dauka na farfado da ilimi a jihar.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, a ranar Talata ya ce, gwamnatin ta ware kaso 31 cikin 100 na kasafin kudin jihar ga bangaren ilimi, ta dauki sabbin malamai, ta gyara makarantu tare da samar da kayan koyo da koyarwa kyauta.
Sanarwar ta kuma kara da cewa wannan nasara ta biyo bayan kokarin gwamnati na inganta ilimin ’ya’ya mata, rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, inganta makarantu, da kuma inganta walwalar malamai.