Ƙungiyar Daliban Nijeriya da ke ƙasar Iraq, NSAI, ta musanta wani saƙon murya da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke zargin cewa ana tura ɗaliban Nijeriya da ke zuwa karatu a Iraq aikin soja ko kuma amfani da su wajen harkokin yaƙi.
A cikin wata sanarwa, ƙungiyar ta ce zargin ba shi da tushe, kuma ba ta samu wani bayani daga hukumomin Iraq ko Nijeriya, jami’o’i ko wasu cibiyoyin da aka amince da su da ke tabbatar da wannan ikirari ba.
NSAI ta yi kira ga ɗaliban Nijeriya da ke Iraq, waɗanda ke shirin zuwa karatu, iyaye, waliyyai da sauran jama’a da su kwantar da hankalinsu, tare da guje wa yaɗa saƙonnin da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.
Ƙungiyar ta jaddada cewa ɗaliban Nijeriya da ke zuwa Iraq ta hanyoyin karatu na hukuma, suna zuwa ne domin karatu kawai, tana kuma ci gaba da sanya lafiyarsu, mutuncinsu da haƙƙoƙinsu a matsayin abin da ya fi komai muhimmanci.
NSAI ta kuma buƙaci jama’a da su riƙa tabbatar da sahihancin muhimman labarai daga hukumomin da abin ya shafa kafin su yaɗa su, tana mai cewa duk wani sahihin bayani da ya shafi ɗaliban Nijeriya a Iraq, za ta fitar da shi ta kafafenta na hukuma.
A ƙarshe, ƙungiyar ta yi kira ga ɗaliban Nijeriya da su kasance cikin haɗin kai, fahimta da taka-tsantsan, tare da ƙin yarda da jita-jita su haifar da fargaba da rudani.
