Sabon Shugaban PDP, Kabiru Tanimu Turaki, Ya Yi jam’iyyarsa ce za ta kafa mulki a 2027.
Shugaban ya bayyana hakan ne a hirarsa ta farko da manema labarai bayan kammala baban taron jam’iyyar na ƙasa da aka gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Don cimma wannan manufar shugaban ya ce, yanzu lokaci ya yi da za a haɗa ƙarfi da ƙarfe don ciyar da jama’iyyar gaba domin Shirye-Shiryen Zaɓen 2027.
“Zan yi iya bakin ƙoƙarina wajen haɗa kan ‘ƴan jam’iyyar musamman waɗanda ke ganin an ɓata musu, don samun nasararta a zaɓen 2027 da ke tafe. Ba zan zuba ido ina kallon masu cin dunduniyar jama’iyar su kai ta ƙasa ba. In ji shi.
Shugaban ya kuma ce, na jami’iyyar PDP su ta yi sulhu ne da waɗanda suke son sulhu.
