
Wani kwale-kwale ɗauke da ‘yan mata guda goma sha daya ya kife a cikin kogin Ningawa dake yankin karamar hukumar Kura.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Juma’ar da ta gabata da misalin ƙarfe takwas na dare.
‘Yan matan ‘yan asalin ƙauyen Godar Dan-Zariya sun taso ne daga garin Kwankwaso bayan sun dawo daga wajen sana’arsu ta sayar da shinkafa.
Sai dai bincike ya nuna cewa daga cikin ‘yan matan da hatsarin ya rutsa da su, 11 sun tsallake rijiya da baya yayin da guda ce ta rasa ranta.
Hakimin karamar hukumar Kura, Alhaji Abubakar Lamido Bayero, wanda Dagacin Butalawa, Alhaji Kabiru Salisu ya wakilta, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai da kuma ‘yan uwan marigayan da suka rasa rayuwar tasu.
Shugaban ƙaramar hukumar ta Kura, Alhaji Rabiu Abubakar Suleman Babina tare da mataimakinsa Alhaji Bello Gambo Kura da sauran jami’an gwamnati sun je garin domin jajanta wa al’ummar garin Godar Dan-Zariya da ma dukkanin mutanen ƙaramar hukumar Kura bisa wannan babban rashi.