
Rundunar Ƴansandan Jihar Jigawa ta ce, ta kama wani mutum mai suna Iliyasu Musa, mai shekara 40, bisa zargin kashe tsohuwar matarsa Hadiza Sale, ƴar shekara 30, a ƙauyen Afasha da ke ƙaramar hukumar Aujara.
A wata sanarwa da kakakinta SP Shi’isu Lawan Adam ya fitar, ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda daga ofishin Aujara ne suka samu nasarar kama shi a ranar Talata, 23 ga Yuli, 2025.
Sanarwar ta ce an kama shi a ƙauyen Larabar-Tambarin-Gwani bayan tsantsan bibiyarsa da suka yi da kuma tura jami’ai na musamman don gano inda yake ɓuya.,
Rundunar ta kuma sanar da cewa mutumin na hanunta, a sashen binciken laifuka da ke Dutse, inda ake ci gaba da gudanar da bincike kafin a gurfanar da shi gaban kotu.
Wanda ake zargin ya shafe sama da makonni biyu yana ɓuya tun bayan da lamarin ya faru a ranar 10 ga Yuli, 2025.
Ana zargin mutumin da kashe matar ne ta yin amfani da sanda sa’ilin da take kan hanyar komawa gida bayan ta dawo daga kasuwa da daddare.