Gwamnatin tarayya ta ce an samu nasarar kama manyan shugabannin kungiyar ta’addanci ta Ansar mutuum biyu.
Mai baiwa shugaban kasa Shawara kan harkokin Tsaron, malam Nuhu Ribadu, wanda ya sanar da haka a Abuja ranar Asabar, ya tabbatar da cewa an kama Mahmud Muhammad Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a, da kuma Mahmud al-Nigeri, wanda ake kira Mallam Mamuda, bayan wani samamen leken asiri.
Ribadu ya bayyana Abu Bara’a a matsayin mai shugabantar ƙungiyar a ƙasar nan, yayin da Mamuda ya kasance mataimakinsa.
Dukkanin mutanen biyu sun samu horo ne a Libya karkashin masu tsattsauran ra’ayi daga ƙasashen waje, kuma sun jagoranci hare-hare da dama a Arewacin kasar nan, sannan sune ke kai wa fararen hula, jami’an tsaro da muhimman gine-gine hari. An danganta su da manyan hare-haren da suka jawo hankalin duniya, ciki har da balle gidan yari na Kuje a 2022, da wani harin a wajen hakar uranium a Jamhuriyar Nijar, sace injiniyan Faransa a Katsina a 2013, sai sace Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba a watan Mayun 2019
.
