Kungiyar malaman makaranta ta NUT ta roki shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya aiwatar da tsarin inganta walwalar malaman makaranta, wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samar tun a shekarar 2020.
Shugaban kungiyar na kasa Audu Amba ne ya bukaci hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai ya yi da shi, a karshen makon nan a birnin tarayya.
Ya ce shekaru 5 ke nan da gwamnatin tarayya ta amince da batun kwaskwarima ga albashin malaman da sauran wasu karin tagomashi garesu don samun karin qwarin qwiwar ci gaba da koyar da dalibai, amma har kawo yanzu shiru malaman suke ji wato alkwarin ya gaza tabbata.
Ya kara da cewa malaman makaranta a yanzu haka babu wanda ya kai su wahala wajen aiki, kuma sune kan gaba wajen samun albashin da ba zai iya biyan bukatun iyalansu ba, kuma hakan yana shafar aikin da suke na koyarwa domin ba yadda za ayi malamin dake cikin damuwar iyali ya samu sukunin iya koyar da dalibi abun daya kamata y akoya.
A don haka ne ya yi kira ga gwamnatin tarayya da jihohi akan su waiwayi malaman don kallo na musamman hakan zai taimaka wajen inganta bangaren koyarwa a makarantun gwamnati dake fadin kasar nan baki daya.
