Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar rashin tsaro a faɗin ƙasar nan, tare da bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an ‘yan sanda da kuma na soji.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa Abdulaziz Abdulaziz, ya bayyana cewa, daukar wannan matakin na daya daga kudirin gwamnatin tarayya domin shawo kan matsalar rashin tsaron a faɗin kasar nan.
Yace shugaban kasar ya bada wannan umarnin ne yayin da yake jawabi a fadarsa a birnin tarayyar Abuja, ya kuma bawa rundunar yan sandan ƙasar nan umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai guda dubu ashirin.
Ya kara da cewa, jami’an da za a ɗauka yanzu haka sun kai 50,000, bayan umarnin da ya bayar na daukar jami’an yan sandan guda dubu talatin.
