Daga Faisal Abdullahi Bila
Hukumar Kidaya ta Najeriya Ntional Populatin Commission NPC ta da hadin gwiwa da shirin FCDO Lafiya sun shiryawa hukumomin gwamnatin jihar Kano da kungiyoyi taron karawa juna sani kan tsare tsaren hukumar wajen samar da ci gaba mai dorewa.
Hukumomin gwamnatin jihar Kano sun hada da ma’aikatar lafiya, al’amuran mata, kididdiga NBS, kasafi da tsare tsare da da kuma kungiyoyi kamar KANSLAM, da ta masu bukata ta musamman.
Kwamishinan hukumar Kidaya na kasa reshen Kano Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa a jawabin sa na kddamar da taron, ya yabawa dukkan mhalarta taron tare da jinjina ga shirin FCDO lafiya saboda cikakkiyar gudunmawar da suke bawa hukumar wajen gudanar da ayyukan ta.
A bangaren sa Daraktan hukumar NPC na kasa reshen Kano Balarabe Kabir ya ce manufar taron na yini uku shi ne wayar da kan jami’an da aka gayyata domin sanar da su yawan al’umar da ake da su a Najeriya da kuma hanyoyin da yakamata a bi domin cin gajiyar yawan al’umar.
Ya kuma ce akwai matsalolin da suka shafi yawan yaran da basa zuwa makaranta, da mace macen mata masu juna biyu da rashin aikin yi tsakanin matasa wanda hakan yasa hukumar ta gayyaci hukumomin da abin ya shafa domin a samar da mafita.
Hukumar NPC ta karrama Dr Abdulkadir Kabara jagoran shirin FCDO Lafiya saboda jajircewar sa wajen tallafawa hukumar.
A jawabin s ana godiya Kabara, ya nuna jin dadin sa tare da alkawarin ci gaba da bawa hukumar gudunmawa a ayyukan ta.
A bangaren sa Maimartaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II wanda maigirma Dankadan Kano Dr Bashir Muhammad ya waklita, yace tsare tsaren da hukumar ta fito da su na ribatar yawan al’umar da ake da su a jihar Kano da Najeriya na da muhimmancin gaske.
Dankadan Kano wanda kuma shi ne shugaban kwamitin lafiya da abinci mai gina jiki na masarautar Kano, ya ce Sarkin Kano Halifa ya damu matuka da ci gaban jama’ar sa musamman lafiyar mata da kananan yara.
A sakon shi na rufe taron, Daraktan hukumar Kidaya na Kano Baba Balarabe Kabir, ya godewa mahalarta taron tare da jan hankalin su da su koyawa abokan aikin su abinda suka koya.
Hukumom da kungiyoyin da suka halarci taron sun bayyana gamsuwa tare da alkawarin za su koyawa abokan aikin su abinda suka amfana daga taron bitar.
Taro ne dai da ya gudana a jihar Kaduna, karkashin jagorancin kwamishinan hukumar Kidaya na kasa reshen Kano Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa d a tallafin daraktan hukumar a Kano Balarabe Kabir, wanda shirin FCDO lafiya karkashin jagoran shirin a Kano Dr Abdulkadir Kabara suka dauki nauyin sa.
