
Hukumar Wayar da Kan Al’umma ta Kasa (NOA) ta jaddada bukatar hadin kai tsakanin al’umma da hukumomi wajen yaki da matsalolin tsaro a yankin Gezawa, Karamar Hukumar Gezawa.
Khadijah Ibrahim Muhammad, jami’a a reshen NOA na Gezawa, ta bayyana wannan bukata ne yayin zagayen wayar da kan al’umma da aka gudanar domin sanar da mutane ayyukan gwamnati da kuma muhimmancin tsaro.
A cikin jawabin ta, Khadijah ta ce zaman lafiya shi ne ginshikin ci gaban kowacce al’umma, kuma ta bukaci al’ummar yankin da su kasance masu lura da duk wani motsi ko hali da ba su yarda da shi ba, tare da kai rahoto ga hukumomin da suka dace domin daukar mataki cikin gaggawa.
Haka kuma, Khadijah ta yi kira ga iyaye da malamai da su kula da ‘ya’yansu musamman a lokacin bikin kammala karatu, tare da yin addu’o’i domin samun nasara da dorewar ci gaban al’umma da yankunan su.
Sanarwar da jami’in yada labarai na shiyyar Gezawa, Jamilu Mustapha Yakasai, ya fitar ta bayyana cewa hukumar NOA ta bukaci a kafa dokar hukunta daliban da suka aikata abubuwan da ba su dace ba yayin bukukuwan kammala karatu, domin tabbatar da zaman lafiya da tsari a cikin al’umma.