
Jam’iyyar (NNPP) ta yi kira ga matasan Arewa da su yi watsi da ikirarin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi na cewa gwamnatin tarayya tana nunawa Arewa wariya.
A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na kasa, Dr. Olaposi Ogini, ya fitar a ranar Lahadi, jam’iyyar ta bayyana zargin Kwankwaso a matsayin marar tushe kuma nufin sa kawai shine tada hankalin jama’a a cikin wannan lokaci mai sarkakiya na kasa.
Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023, ya zargi gwamnatin Tinubu da nuna wariya ga Arewa ta fuskar ayyukan tituna. Sai dai NNPP ta karyata wannan zargi, tana mai cewa Kwankwaso yana kokarin rura wutar fitina.
Sanarwar ta ce: “NNPP tana kallo da matukar damuwa kan wannan furuci na Kwankwaso na ikirarin ware Arewa a karkashin gwamnatin Tinubu wanda bai da wata hujja,.”
Jam’iyyar ta kara da cewa tarihin Kwankwaso na yin furucin da ba a tabbatar ba, ya sa aka kore shi daga NNPP. Jamiyyar tace irin wadannan ayyuka na sa jam’iyyar shiga shari’o’i
Jam’iyyar ta yi kira ga matasan Arewa da su binciki ayyukan raya kasa na gwamnati da kansu tare da kuma duba ayyukan Kwankwaso a lokacin da yake a mukaman gwamnati, ciki har da lokacin da ya ke sanata, minista da gwamna.
