
Wanda hakan zai sa ‘yan majalisar dokoki na jam’iyyar za su sauya sheka zuwa APC in ji shugaban Jamiyyar na kasa
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi hasashen rugujewar Jam’iyyar NNPP da kuma sauya shekar wasu ‘yan majalisar dokoki na jam’iyyar NNPP.
Ganduje ya yi wannan furuci ne ranar Lahadi a taron APC da aka gudanar a Kano a inda kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau I. Jibrin, ya raba motoci da babura ga mambobin jam’iyyar.
“NNPP jam’iyya ce da ke gab da rugujewa, don haka manyan jiga-jigan ta da ‘yan majalisa za su tsere zuwa APC.
“ Ganduje ya jaddada cewa, “APC na ci gaba da karɓar sabbin mambobi daga NNPP”. In ji shi.
A makon da ya wuce ne wani dan Majalisar Walkilai na Jam’iyyar NNPP ya sauya sheka zuwa APC a infa ya samu babban tarba daga shugaban Jam’iyyar APC a Abuja
