
Majalisar kula da harkokin shari’a ta kasa (NJC) ta dakatar da wasu alkalai uku na tsawon shekara daya ba tare da biyansu albashi ba, sakamakon samun su da aikata wasu manyan laifuka da suka saba ka’idar aiki.
Majalisar ta dauki matakin ne a yayin zamanta karo na 108 da aka gudanar a ranakun 29 da 30 ga Afrilu, 2025, a karkashin jagorancin shugabar Kotun Koli ta Kasa Justice Kudirat Kekere-Ekun.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na majalisar, Kemi Ogedengbe, ya fitar a ranar Laraba da dare, ya ce, an dauki matakin ne bayan kammala bincike mai zurfi kan koke-koken da aka gabatar.
Alkalan da aka ladabtar sune Mai shari’a Jane Inyang ta kotun daukaka ƙara dake Uyo, wadda aka samu da laifin amfani da matsayinta wajen bayar da umarnin da bai da tushe wajen sayar da wani gidan mai da wasu kadarori na kasuwanci da ke cikin wata shari’a da take jagoranta.
Da Mai shari’a Inyang Ekwo na Kotun Tarayya dake Abuja da ya gamu da aka tabbatar da koke-koke masu tushe kan hukuncin da ya yanke a wata kara ba tare da sauraron dukkan bangarori ba.
Baya ga dakatar da shi na shekara daya ba tare da albashi ba, an hana shi daukaka zuwa wani matsayi mafi girma har na tsawon shekaru biyar.
Sai kuma Mai shari’a Aminu Baffa Aliyu na Kotun Tarayya a jihar Zamfara da aka dakatar tsawon shekara guda ba tare da albashi ba, bayan da aka gano laifukan cin zarafin ka’idojin shari’a da suka shafi yadda yake gudanar da aikinsa.
Majalisar ta NJC ta bayyana cewa irin wadannan matakai na daga cikin kokarinta na tabbatar da gaskiya, amana da kwararru cikin tsarin shari’ar Najeriya.