
Hukumar Kula Yanayi Ta Kasa NIMET, ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama hade da tsawa a wasu sassan kasar nan daga yau Lahadi zuwa Talata 11 ga watan Yunin 2025.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar a ta raba wa manema Labarai, Inda ta ce za a iya samun wannan yanayin a sassan da suka hadar da yankin Arewa maso yamma, Arewa ta Tsakiya, da wasu yankunan a Kudancin kasar.
A cewar NiMet, ana sa ran ranar Lahadi za a fara da ganin gajimare a wurare da dama, amma zuwa yammacin ranar yanayi zai sauya.
Daga cikin jihohin da zasu iya fuskantar hakan a cewar hukumar sun hadar da nan Kano, sai katsina, Taraba, Adamawa, Zamfara, Kaduna, Jigawa, Borno, Gombe, da Bauchi.
Sauran sun hadar da babban birnin tarayya, Neja, Nasarawa, Kwara, Kogi, Benue da Plateau da sauransu.
Hukumar ta kara da jan hankalin alumma akan su tabbatar da sun yashe magudanan ruwan su, don hakan zai taimaka wajen kaucewa ambaliya.
